Spread the love

Sarkin Bama a jihar Borno Kyari ibn Umar El-Kanemi ya bayyana cewa yankinsa gaba daya ba wurin zaman karuwai ba ne domin yana son kwanciyar hankali da zaman lafiyar yankinsa.

Malam Abba Shehu Umar Sakataren Sarkin ya fitar da bayanin ga manema labarai ya ce Sarkin yayi wannan jawabin ne a sakonsa na murnar Mauludi na shekarar 2019, Sarki ya nuna bacin ransa yanda yawan Karuwai suke a yankin bayan rufe gidajen masha’a a Unguwar Galadima cikin birnin Maiduguri.

A cewarsa an fara samun rashin tarbiya tun lokacin da matan suka dawo yankinsa, don haka masarauta ba za ta lamunce aiyukkan badala da karuwan ke aikatawa ba.

Ya ce suna iya tunawa matan su ne ake samu cikin aikata manyan laifuka irin safarar yara, tu’amali da miyagun kwayoyi da sauran abubuwan laifi a cikin birni. Kan haka gwamnati ta dauki matakin rushe wuraren masha’arsu. ‘Bayan nan ne suka watsu cikin kananan hukumomi, abin da ba za mu yar da shi ba, na umarci kananan hakimaina su kula kar su bari a rika yi wannan muguwar dabi’a a wurinmu’ a cewarsa

Ya ce duk wadda suka kama tana karuwanci za su kai ta ga hukuma a hukunta ta su rushe in da take zaune  kamar yadda tsarin gwamnatin Borno ya tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *