Hukumar kula da abinci da magunguna ta Kasa(NAFDAC) ta ce ta tabbatar da kashi 60 na maganin da ake shigowa da shi Nijeriya ba kamfanoni ake yinsu ba, wadan da ake yi ne a gidaje.

Babbar Darakta a hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce a wurin taron manema labarai da ta gudanar a Abuja.

Ta ce akwai bukatar tashi tsaye don ganin an tsaftace shigowa da maganin da ake yi na gida. Ta kara da cewar yawan maganin da ke cikin kasar yana cikin abin da ke kawowa kasar ci baya.

Ta ce muna son shiga da kula wuraren yin maganin, kashi 60 na maganin dake shigo mana ya zama an kawar da su a kasar nan, sai mu a nan Nijeriya mu rika samar da namu.

Muna iya karfafa masu yin magani a kasar mu su rika yi amma da sanin hukuma duk mai bukata ya zo ya zauna da hukuma ba wai ya yi gaban kansa ba shi ne abin da ba mu gamsu da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *