Mutum dubu ashirin da tara ne ke neman gurbin aiki dubu da dari biyar na karanatarwa a makarantun gwamnatin jihar Ogun Gwamna Dapo Abiodun ne ya sanar da hakan.

Gwamnan a jawabinsa da sakataren yada labarai Kunle Somorin ya fitar ya ce mutum 1,500 ne suka nemi aikin ta hanyar kaitsaye ga gwamnati.

A cewarsa gwamnati fara duba wadanda za ta doka bayan ta rufe karbar takardun neman aikin a ranar Assabar data gabata.

Gwamnan ya ce daukar wasu malamai ya zama dole domin inganta haujin ilmi a jihar, gwamnati ta himmatu ta samar da kyakkyawan yanayi a haujin karantarwa za ta sake gyara dukkan makarantun dake mazaba 236 a fadin jihar.

Ya ce adadin makarantu 90 ne aka gyara, wasu yanzu haka ana kan gyaransu a yi masu rufi da sanya musu kujeru yanda makarantun za su zama masu inganci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *