Spread the love

 Maidakin Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto Hajiya Hafsat Manir Muhammad Dan’iya ta Kaddamar da shirin Soma Koyar da matas Mata da maza Sanaoin Hannu don dogaro da akai a karkashin Gidauniyarta  

Shirin da aka soma a karamar hukumar Kware   zai game dukkan Mazabu 11 dake akwai a wananan Karamar Hukumar  yanzu dai za a soma Mazabar Gidan Karma.

“Ita dai wannan Gidauniya Mai suna  Gidauniyar Hafsat Manir Dan’iya an kafa ta ne da zimmar fitowa da shiruruwa da za su inganta rayuwar Mata da Kananan yara, kai harma da maza matasa, don dogaro da kai da kuma samar ma alumma hanyoyin yaki da talauci. Ta hanyar shirya horo da fito Sabbin hanyoyin sana’o’in da arzikin mutum ke bunkasa nan da nan,  domin a sauya  tunanin Mata da matasa maza daga zaman banza ko zama cima kwance, Wanda su ne ummul haba’isin Shiga halaye na banza da ke kai alumma ga halaka.”

“ Mutane 15  Mata 10 Da Maza 5 ne  daga Mazabar Gidan Karma  za su koyi sanaoi daban -daban don dogaro dakai da Za’a  Koyar da su  a Wananan Cibiyar da aka bude a Garin Kware a karkashin wannan Gidauniyar inda Mata za’a koya masu sana’o’in dunki, sakar tufafi  na zamani, yin Tokar wanka da Man shafi, Mazan  za’a koya masu Sana’o’in yin Takalma Wanda zai dauke su Watanni 2 ana koya masu a cikin Cibiyar.  Bayan sun Kammala Za mu sake dawowa don yin bukin Yaye su,da kuma basu tallafin Jari don cigaba da yin sanao’in da suka koya don taimakon kai da kai.” Kamar yadda maid akin Mataimakin gwamna ta ce a jawabinta ranar bude ciyar.

Da farko Uwargidan Gwamnan jihar Sokoto Hajiya Mariya Aminu Waziri Tambuwal ta gode wa Hajiya Hafsat ga irin wannan namijin aikin da ta fito da shi domin taimakon al’ummarta abu ne da yakamata diuk wata mai kishin jihar ta fito da shi domin kara taimakon shiraruwan gwamnati.

Hajiya Mariya a tabakin wakiliyarta Kwamishiniyar ilmin Kimiya ta jiha Dakta Kulu Abubakar ta ce da za a rika samun mutane na tunanin taimakon al’umma ga abin da suke da shi da an samu cigaba fiye da yanda ake ciki yanzu. Ta yi fatar gidauniyar ta dore da cigaba da taimakon al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *