Spread the love

Ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar masu cutar shuga a jihar Sokoto Hajiya Rakiya Garba Kilgori ta shirya taron wayar da kai na yini ɗaya ga masu cutar shuga a jihar domin sanar da su abincin gida da za su riƙa ci ga wanda baya da zarafin sayen manya abincin masu shuga dake da tsada.

Kilgori ta ce can baya gadon ciwon ake yi amma yanzu ba haka ba ne ƙaramin yaro ko yarinya sai ka gansu da ciwon dole ne mu tashi tsaye mu faɗakar kan abincin gida da mai ciwo zai iya cinsa bai yi masa lahani ba.

A wurin taron da aka samu halartar mutane kusan 200 wadda ta shirya taron ta yi bayanin kan maƙasudin kiran masu fama da cutar ta ce ku sani ni ɗaya ce daga cikinku duk abin da kuke ji na ciwo da wahalarsa na sani kan haka ban da ƙudiri kamar na taimaka muku..

Bayan mun sanar da hukumomin duniya kan abincin gida da muka ga masu ciwonmu na iya ci sun amince har Suka ba mu damar mu zo gwadawa jama’armu abincin da yanda za a ci a sauƙaƙe. Fatana in riƙa taimakawa al’umma musamman masu wannan ciwo, akwai shirin faɗaɗa wayar da kan zuwa ƙauyukkan jihar. A cewar Rakiya Kilgori.

Jami’in lafiya Muhammad Waƙili Dange ya jinjina wadda ta shirya taron da fatan mahalarta za su fahimci abin da za a faɗa musu kuma su sa shi a aiki don kare lafiyarsu ga wannan ciwon mai kisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *