Spread the love

BUDURCI NA WUCCIN GADI KO KUMA Artificial Virginity Hymen a turance.


Da akwai Wani Budurci na Wuccin Gadi da Ya Shigo a Nigeria tun Kusan Shekarar 2015, ta In da Idan Macce ta Rasa Budurcin ta a Waje Idan zata yi aure sai ta saye shi ta sanya (ta yanda Za’ayi wa Mijin Basaja), kuma Alhamdulillahi Mun fad’akar a wancen lokaci game da Wannan Budurci.

Sai dai kuma yanzu abin ya k’ara hab’aka ta In da Suke da Web Site Wanda Idan Macce tana buk’atar Wannan Budurci zasu Iya samunta duk In da take a Nigeria su kai mata shi tare da koyar da Ita yanda ake amfani da shi.

HYMEN a turance wata fatace datake gaban mata dab da cervix, a hausance tana daukan sunan BUDURCI, kuma rashin (wannan fatar shine rashin budurci).

Fatar bata da karfi sosai domin ruwa kan iya wucewa ta cikinta, wannan fatar tana dauke Da kananan hanyoyina jini, shiyasa fashewa ko tsagewarta kansa jini ya fita.

Mafi akasari wannan fata kan tsage ne idan daya daga cikin wadannan abubuwa ukku suka faru ga macce:

  1. Idan an sadu da mace (wanda ake kira copulation a turance)
  2. Wajen neman fitar da sha’awa da wani abu mai karfi ko yatsa (vaginalinsertion or mastubation)

3.Yawan tsalle ko hawa mashin, keke, doki ko jaki. Duk sukan iya fashe wannan fatar.

Kasancewa mafi yawan Maza kanyi amfani da fashewar wannan fata da fitar jini wajen gwada budurcin ‘Ya mace don tabbatarwa bata ta6a saduwa da ko wane namiji ba, Sai turawa suka zauna sukayi nazarin yin Jabun wannan Fatar (mai suna Artificial Virginity Hymen) domin matan da suka rasa budurci kafin Aure.

Shi wannan FAKE HYMEN roba ce da akayita da sinadare masu narkewa dazai dace da jikin mutum (prosthetic in nature) yanda idan macen da ta rasa budurcinta tasa zai zauna daidai gurbin ta, sannan da zarar ta sadu da angonta wani jan sinadari zai fashe daga cikin Artificial Virginity Hymen din mai kama da jini, toh dazarar ango yaga haka sai ya zaci matar sa budurwa ya aureta.

Babu shakkah akwai abubuwanda ya kamata mata su kula da su game da wannan Fake Hymen din.

Kasancewar bayan saduwa fake hymen zai iya fitowa, in kuma bai fito ba zai iya narkewa a cikin gaban mace, don haka zai iya kawo matsalolin lafiya ga macen datayi amfani dashi.

Haka zalika jan ruwan da wannan FAKE HYMEN din ke fitarwa mai kama da jini, shima zai iya canza ka’idar tsaftar gaban mace, saboda cikinsa akwai (chemicals) masu dauke da kalar JA, don haka wannan abin zai iya kawo matsaloli kamar haka:

Yana canza yanayin sinadaran dake kiyaye al’aurar Macce daga kamuwa da cutukka. Yana iya kawo cancer of vagina. Yana toshe mahaifa akasa samun haihuwa. Yana canza tsarin hailar mace (ta yanda hailar zata rikice).

Sannan dadin dad’awa wannan fake Hymen din Yana kawo rashin haihuwa (infertility) ga mazan da sukayi amfani da wacce ta sanya shi.

Don haka yana da matuk’ar kyau matayenmu su guji yin Amfani da Wannan Fake Hymen din.

Sannan Yana da Kyau Malamai su tashi tsaye Wajen Yin fad’akarwa akan Cewa, Rashin Ganin Jini a lokacin Saduwa da Macce da Angonta ba shike nuna ta yi amfani da wani a waje ba.

Sannan Muma Maza Mu san Cewa, rashin ganin Jini a daren Farko bashi ke Nuna Cewa Macce ‘yar Iska bace. Domin Mu samu matayen mu hankalinsu ya kwanta kar su kai kawunansu ga Halaka.

Mu san Cewa, Tsallaka Rami ko Hawa Keke, ko Hawa babur kad’ai na iya Farke wannan Hymen d’in din ba dole sai Macce ta sadu ba.

Kai Hatta dogon Numfashi Idan macce tayi Shi Zai iya sanya tayi hasarar wannan Budurcin, a likitance ma an gano cewa, akwai matan da masu da ma shi. Don haka mu tashi tsaye domin yak’ar wayannan yahudawa da suke yak’ar mu a b’oye.

Mai Aikata Alkheri Yafi Alkheri Alkheri a Cikin Al’ummah don haka Over to you Inji Turawa (ya rage naku ko ku turawa ‘yan Uwa ko ku barsu a Cikin Duhu).

Allah ya kyauta

Mashkur Abdullahi Tsafe
Health educator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *