Spread the love

Gwamnan Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci tawaga domin tattaunawa da bankin cogaban musulunci dake Jidda daga nan za su wuce ƙasar Amerika domin ganawa da Bill Gates da Aliko Ɗangote shugaban gidauniyar Milinda da gidauniyar Ɗangote.

‘Gwamna baya gari, mataimakinsa Manir Muhammad Ɗan iya ne zai zama muƙaddashinsa.’

A ranar Assabar suka tafi ƙasar Saudi Arebiya domin ganawa da mutanen banki kafin wucewa Amerika kan lamurran kiyon lafiya, ilmi, samar da kuɗin yin gine-gine hoɓɓasawa ce mai kyau ga gwamna Tambuwal.

Gwamnan ya ce tattaunawarsu da bankin cigaban musulunci ba da daɗewa ba Sakkwatawa za gani a ƙasa.

A tattaunawar gwamna da manyan masu kuɗin nan za a dubi abubuwan cigaba a fannin ilmi da ruwan sha, musamman samar da yanayi mai kyau a gefen karatu da karantarwa a ƙarƙashin gidauniyoyin.

Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai Muhammad Bello ne ya fitar da bayanin tafiyar ya kuma nuna juhar a yanzu tana hannun mataimakin gwamna duk ba a bayyana ko an sanar da majalisar dokokin ji ba.

‘Gwamna baya gari, mataimakinsa Manir Muhammad Ɗan iya ne zai zama muƙaddashinsa.’

A bayanin ba a bayyana yawan kwanakin da gwamna zai yi a wannan tafiyar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *