Spread the love

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sallamar hadiman mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo, an ba da dalilin ɗaukar matakin da cewa saboda a ragewa geamnati nauyin da ke samanta ne aka yi hakan.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya ce a wani jawabi da ya fitar rage mutanen yana cikin ƙoƙarin da ake yi na saka wa mutanen da suka sha wahala a kakar zaɓen bana.

Mataimakin shugaban ƙasa yafi ogansa yawan hadinmai ga kuma ana son rage yawan hadimmai a fadar shugaban ƙasa.

Ya ce rage mutanen ba yana nufin ana da matsala da Osinbajo ba, shugaban ƙasa ke jagorantar mulkin ƙasar nan. Manema labarai su bar ƙirƙirar abin da babu suna danganta shi da wani. Buhari ne cikakken mai mulki.

Wannan lamarin yana cikin ƙudirin Buhari na rage yawan kuɗin tafiyar da jagoranci a hukumomin gwamnati.

Fadar ta ƙaryata rashin jituwa da ake cewa akwai tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa, dangantkarsu mai kyau ce akwai yarda tsakaninsu.

A cikin jerin hadiman da aka kora daga biyar ne kawai Hausawa sauran 30 suna cikin ƙabilun ƙsar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *