Spread the love

Ɗan shekara 22 Ibrahim Magaji a ƙauyen Ƙosawa ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano ya bugi Auwalu Hussain har ya mutu domin ya haski budurwarsa da fitila.

Magaji ya je fira wajen budurwarsa a ƙauyen Dakasoye dake ƙaramar hukumar Garun Malam a ranar Lahadin da ta gabata lokacin al’amarin ya faru.

Wanda ake zargin yana tsaye gaban budurwarsa sai margayin ya zo ya haski fuskarta da fitila, abin da ya gani an ci zarafinta sai ya ɗauki wannan mataki mummuna.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da sun kama wanda ake zargin, kuma yanzu haka suna kan binciken wanda ake zsrgin da yin wannan aika-aikar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *