Hana sayar da man fetur a garuruwan dake kusa da boda zai jefa su cikin ƙuncin rayuwa

Hukumar kwastam ta bayar da umarni da gaggawa abar dayar da Man fetur a gidajen man dake kusa ga bododin Nijeriya duk gidan man da bai kai kilomita 20 tsakaninsa da kan iyakar ƙasa da ƙasa a rufe shi.

Abinciken da Managarciya ta yi ta gano akwai ɗaruruwan gidajen mai a kusa ga bododin Nijeriya da chadi da Nijar da Kamero da wannan umarni zai shafa.

Mutanen dake cikin garuruwan sun yi magana kan lamarin sun ce umarnin zai shafi rayuwa da tattalin arzikinsu. Amma su kwastam sun ce an yi haka ne domin hana sumogalin ɗin man fetur a waɗan nan ƙasashe.

Al’ummar sun koka sosai ganin yanda komi ya tsaya harkoki ba su tafiya yanda yakamata man fetur shi ne ginshiƙin komai a sha’anin tafiyar harkoki.

Gwamnati ta duba wannan lamari bai kamata ta wahalar da mu ba muna cikin ƙasarmu ta gado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *