Spread the love

Majalisar dattijan Nijeriya ta sake gabatar da dokar nan ta tsaftace dandalin sada zumunta na zamani a Nijeriya in da take kokarin yin dokar shekara uku gidan yari ga duk wanda ya wallafa labarun karya a dandalin sada zumunta na zamani

Wannan dokar ana son yin ta ne ga masu saba dokar yada labarai da buga labarun karya a yanar gizo.

Daftarin dokar yana cikin guda 11 da aka gabatar a zauren majalisar domin zama doka a shekarar 2019.

An yi wa daftarin karatu na farko, wanda ya gabatar da kudirin ya ce akwai bukatar yin haka domin hadin kan kasa baki daya

Ya ce yin dokar ba yana nufin hana mutane shiga yanar gizo su yi abin da suke so wanda bai sabwa doka ba, amma duk wanda ya yi amfani da kafar ya fadi labarun karya saboda ya cimma wani burinsa. doka za ta hukunta shi, in da zai yi shekara uku gidan yari ko ya biya tarar dubu 150 duk wanda aka kama da ya aikata laifin.

Wuraren da ake saka labarin matukar suka bari an sanya labarun karya ba su dakatar da mai yi ba za su biya tara tsakanin miliyan 5 zuwa 10. domin sun fi laifi da suka ki dakatar da sanya labarun karya a wurinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *