Spread the love

Kamfanonin raba wutar lantarki a Nijeriya an ba su zuwa 7 watan Disamba su miƙa rahotonsu da zai fito da bayanai ƙarara kan dalilin da suke ganin bai kamata gwamnati ta soke takardun lasisinsu ba. Suna son a barsu su cigaba da raba wutar lantarki a Nijeriya. Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa  (Nigerian Electricity Regulatory Commission) ta sanar da ƙarin wa’adin.
A wasu takardun bayanai da kamfanonin suka gabatar wa hukuma kan ƙorafinsu a wurin wani ƙaramin zama da aka yi Abuja don a duba makamar lamarin an ƙara sanar da hukumomin abin da ake saran su yi kafin lokacin miƙa bayaninsu.
Hukumar ta fitar da sanarwar ƙudirinta na soke kamfanonin raba wutar lantarki da aka fi sani da (DISCOS) su takwas daga watan Okotoban wannan shekara, sai dai ta nemi su kare kansu cikin kwanaki 60 in ba su yi haka ba za a soke Lasin ɗinsu.Kamfanonin su takwas su ne   Abuja, Benin, Enugu, Ikeja, Kaduna, Kano, Port Harcourt da Yola Discos.
A cewar hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa NERC kamfanonin raba wutar Discos, sun saɓawa ƙa’idojin rabon Lasin kamar yadda tsarin dokokin wutar lantarki ya sanar wanda aka yi wa gyaran fuska a  2016 – 2018. An dubi dokar sanya kuɗin wuta da bayar da su. 
Abin jira a gani in sun kasa gamsar da gwamnati za a soke lasisinsu ne ko za a ƙara ba su wa’adi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *