Spread the love

Kusan mutum miliyan 4.02 na ‘yan Nijeriya mafi yawansu daga jihohin Borno, Yobe da Adamawa ake sa ran za su fuskanci katsewar abinci, matsalar ta rashin abinci za ta fara ne daga yanzu har zuwa watan Disamban 2019, kamar yadda rahoton masana kan wadatuwar abinci suka bayyana.

Sun ce jihohi 16 ciki har da Abuja za su fuskanci matsalar. Ƙungiyar manoman abinci a wurin taro fitar da bayanin Okotoba ne suka faɗi haka a Abuja.

Rahoton ya ce mutanen Nijeriya miliyan 5.94 ake tsammanin su faɗa cikin matsalar tsananin rashin abinci daga watan Yuli(june) da Agustan shekarar 2020.

Hasashen na masanan ya bayyana jihohin da za su shiga matsalar su 16 da suka haɗa da Adamawa,Bauchi,Benue, Borno, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Neja, Filato, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da Abuja.

Waƙilin ƙungiyar a Nijeriya Mista Sufyan Koroma ya ce aikin na bincike sun fara shi tun shekarar 2015 sun shigo da masana harkar abinci abin da ya kawo aka yi gargaɗi domin kare matsalar.

Yaƙin Boko haram da wasu abubuwan ta yarda ƙayar bai ana ganin sun bayar gudunmuwa ga samun matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *