Tsohon Gwamnan jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje ya yi kira ga shugaba Buhari da ya shiga tsakani domin warware matsalar da ta kunno kai tsakanin jihar Gombe da Bauchi kan hakkin mallakar rijiyoyin man fetur da aka gano kwanannan a yankin.

Sanatan ya yi kiran ne a Gombe lokacin da yake jawabi ga sabbin kwamishinonin da za a nada da manyan sakatarori da masu baiwa gwamna shawara, a wurin taron sanin makamar aiki da aka shirya masu.

Kamfanin Mai na NNPC a kwanannan ne ya sanar da samun dayen man fetur a kan iyakar jihar Gombe da Bauchi a gulbin Kolmani.

Goje ya ce samun Man fetur a Arewa ta Gabas, Arewa ce gaba daya yakamata a kalle shi a matsayin cigaba ne aka samu abu ne da zai kara kawo hadin kai da wanzuwar kasa daya don a yanzu za a samar daidaito a rabon kudin kasa da yawan samun kudin shiga.

Ya yi kira ga shugaba Buhari yi yi gaggawar shiga tsakani ya warware matsalar a san rijiyoyin suna cikin karamar hukumar Akko ne ta jihar Gombe ko suna cikin karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *