Spread the love

Mutum bakwai ne suka rasu bayan da jirgin ruwa ya birkice da mutane a gulbin Gwayaka da ke yankin cigaban Lafiya ta Gabas a jihar Nasarawa.

Lamarin ya zo ne shekara daya bayan wasu mutum hudu sun rasa ransu a wani hadarin jirgin ruwan cikin Ashangwa dake cikin yankin.

Shedun gani da ido ya sanar da cewa wadanda lamarin ya rutsa da su mafi yawansu manoman rani ne daga jihar Kano suna kan hanyarsu ta komawa ne daga gona lokacin da lamarin ya faru.

A cewarsa karamin jirgin ruwan na katako ya kwashi abin da yafi karfinsa ne sama da mutum 20 suka shiga jirgin da kayansu matukin ya bukaci su rage an yi wa jirgin yawa, wasu su bari ya je ya dawo zai yi sawu biyu suka ki

Matukin ya yi fushi ya fita daga cikin jirgin, daya gada cikin Fasinjojin ya sanya sandar tukin jirgin ya fara tafiya da ‘yan uwansa suka ratsa gulbin, kafin su an kara jirgin ya tuntsure da su a tsakiyar gulbi, mutum bakwai ba a san in da suke ba, sauran sun fita da ransu. a cewar wanda aka yi gabansa

Ya ce an gano gawar mutum uku a ranar Litinin in da har yanzu ba a ga sauran ba amma ana kan bincike a gano sauran hudun.

Mai kula da yankin cigaban garin Lafiya ta gabas Shu’aibu Dahiru Zanwa ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna kan kokarin a samo sauran gawar da ba a gani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *