Spread the love

Gwaman Babagana Umara Zulum ya ba da sanarwar gwamnatinsa za ta bayar da tallafin miliyan 50 domin saukakawa ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa masu sayar da wayoyin hannu da suka yi gobara a kasuwar waya ta cikin Maiduguri.

Kasuwar ta kama da wuta a ranar Alhamis data gabata da dare a lokacin gwamna ya yi tafiya cikin tawagar shugaban kasa zuwa kasa mai tsarki. Bayan ya dawo ne ya kafa kwamiti da yake jiran rahotonsu da za a bashi ranar juma’a ya ga irin hasarar da aka yi domin soma ba su kudin.

Daga Filin jirgi gwaman bai tsaya ko’ina ba sai kasuwar ya ce yana jajantawa wadan da lamarin ya faru gare su ya godewa jami’an kashe gobara da jama’ar da suka taimaka aka kashe wutar.

Bayan ya duba yadda wutar ta ci ya ce wurin yana cunkoso sosai gwamnati za ta duba yiwuwar sauya masu wani wuri domin kara inganta kasuwancin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *