Kungiyar dilolin kayan wutar lantarki a kasar Ghana ta rufe shagunan ‘yan Nijeriya 50 kan sabawa dokokin cikin gida da suka yi.

Akalla shhaguna 50 aka rufe na mutanen Nijeriya a babbar masana’antar Opera a tsakkiyar birnin Akkara.

Kungiyar a satin da ya gabata ta aika takardar bayani ga duk wanda ba dan asalin Ghana ba, ana sanar da shi ya fita daga cikin shagunan da yake ciki daga 4 ga Nuwamban nan.

Mai magana da yawun kungiyar Samuel Addo ya ce matakin yana kunshe cikin sashe na 27(1) a tsarain doka ta 865 na harkokin kasuwancin Ghana, na baiwa ‘yan kasa muhimmanci a kasuwanci.

Mambobin kungiyar sun zo a shagunan ‘yan Nijeriya dake cikin masana’antar da aka kori ‘yan Nijeriya sun samu sun rufe shagunansu da makulli.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na kasar Ghana Chukwuemeka Nnaji ya kwantar da wutar ya kai maganar hannun ‘yan sanda.

An samu kwanciyar hankali a kasuwar komi ya fara daidaita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *