Spread the love

Jarumar fim ɗin Hausa Ruƙayya Umar Santa da aka fi sani da Dawayya ta ce su ‘yan fim yakamata su riƙa fitowa zaɓe ba wai goyon baya ba.

“Mu Ya Kamata Mu Tsaya Takara A Zabe Mai Zuwa, Saboda Mu Muka Fi Kowa Farin Jini, ‘Yan Siyasan Ma Da Mu Suke Taƙama”. Inji Jarumar Finafinan Hausa, Rukayya Dawayya.

Jarumar tana ganin farin jininsu zai sa su ci zaɓe tun da suna yi wa ‘yan siyasa waƙa da yawon kamfe.

Tunanin jarumar yana da kyau su gwada zai fi don a lokacin ne za su gane yanda mutane suke kallonsu, ta manta sanda Nura Hussain ya yi takara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *