Spread the love

Fitaccen malamin addinin musulincin nan a Najeriya, kuma ministan sadarwar kasar, Sheikh Ali Isa Pantami ya ce ya yaba da yadda fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon ta roki Allah gafara kan wata “katobara” da ta ce ta yi a shafin Twitter ranar Lahadi.
Gabon dai ta mayar wa wani mutum martani ne a shafin Twitter wanda ya zage ta a wani hotonta dana ƙawayenta abokan aikinta Rahama Sadau da Fati Washa da Rahamar ta wallafa a Twitter.
Wannan abu da Hadiza ta yi dai ga dukkan alamu ya burge ma’abota shafukan sada zumunta da muhawara a Najeriya, inda daga wallafa sakon da misalin karfe 5:58 na yammacin Lahadi zuwa 9:30 na safiyar litinin an sake yaɗa shi sau 638 an kuma so shi sau 3,600 sannan wadanda suka bayar da amsa ga sakon suna da dumbin yawa.
Za a iya cewa kashi 95 cikin 100 na wadanda suka ba da amsa sun yabe ta ne kan tuban da ta yi, amma duk da haka akwai ‘yan tsiraru da ke ganin cewa “aikin gama ya gama, ta makaro, abin da suke ganin ya nuna zahirin wace ce ita.”
Sakon nata ya ce: “Astaghfirul Laah kan martanin da na mayar marar kyau kan wata amsar rashin da’a da wani ya ba ni. Na goge sakon kuma na nemi gafarar Allah kan kokarin mayar da martani cikin fushi kan wani kuskuren da aka yi.”
Ministan Sadarwa na Najeriya kuma fitaccen malamin addini Sheikh Isa Ali Pantmi ma ya bayar da amsa a kan sakon Hadiza Gabon.

Saƙon ministan dai na cewa ne “Wannan babban abun a yaba ne a nemi gafarar Allah bayan yin wani kuskure. Allah Madaukakin Sarki ya yafe mana ya kuma yi mana jagora tare da kare mu a gaba.”
Sai dai shi ma ministan ya sha martani daga wasu mabiya Twitter din inda wasu ke cewa me ya kawo shi cikin wannan maganar, yayin da wasu kuma ke yaba masa.
Hoton dai ya jawo ce-ce-ku ce a shafukan sada zumunta musamman na Twitter da Instagram inda dukkan jaruman suka sanya a shafukansu.
Wani matashi ne ya fara cin zarafin jaruman inda ya zarge su da yin zina kafin su dauki hoton. Ba da jimawa ba ne ita kuma Hadizan ta mayar masa da martani da cewa da mahifinsa ma suka yi zinar.
Tuni dai Hadiza ta goge wannan sako ta kuma wallafa wani na neman gararar Allah SWT da yin da na sanin mayar da wancan martanin tun da fari.

Ainihin hoton da ya jawo ce-ce-ku ce din
A ranar Asabar ne Rahama Sadau ta wallafa hoton mai dauke da ita da Hadiza Gabon da Fati Washa a shafin Twitter inda ta yi masa take da “ma ki gani ya kauda idonsa”.
Sannan ta sake wallafa irinsa a shafin Instagram inda kuma nan da nan hotunan kala uku suka yadu kamar wutar daji.

Sun dauki hoton ne a birnin Landan yayin da suka je karbar wata karramawa da aka yi musu.
Shaikh pantami yana bibiyar shafin masu shirya fim kenan da har yake tanka musu ga batutuwansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *