Spread the love

Daga Dooshima Abu
BBC, Abuja.

Za ku iya mamakin yadda yarinya ‘yar shekara 15 kacal da ke gararamba a Abuja ke kwanciya da maza 15 domin kawai ta biya bashin da ake bin ta.

Wannan ne irin mummunan halin da Ngozi (Sunan da muka ba ta) ta kwashe watanni tana fuskanta a wani otel da ke unguwar Lugbe a Abuja.

Ngozi ta fada wannan hali ne bayan da wata makwabtciyarsu a wani kauye da ke jihar Anambra ta yi mata alkawarin taimaka mata ta hanyar biyan kudin makaranta idan ta biyo ta zuwa Abuja.

Ta ce “Madam takan umarce ni da sanya guntun siket da karamar riga. Nakan kwanta da maza 15 a naira 1000 kan kowane mutum, nakan hada 15,000 a kowace rana domin biyan ta bashi.”
Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya NAPTIP ta ce kimanin kashi 75 na yara irin su Ngozi da ake fatauci daga wata jiha zuwa wata, a Najeriya, suna fadawa ne hannun miyagun mutane.

Matashiya ta cinna wa kanta wuta a Zamfara saboda soyayya
‘Sanin sirrin karuwanci ya sa nake kyamarsa’
Mercy (Wadda muka canza wa suna) na daya daga cikin irin su.

Ita ma ta shaida wa BBC cewa an yaudare ta ne aka kai ta otel din da aka kai Ngozi, a unguwar Lugbe da ke Abuja.

Ta ce ta yi yunkurin guduwa bayan ta kwashe watanni tana yi wa wadda ta kawo ta bauta, amma sai matar ta kama ta, inda ta yi amfani da reza wurin tsattsaga mata jiki.

Akwai gidajen karuwanci na kananan yara da yawa a Lugbe
Wurin da wannan otel yake a unguwar Lugbe da ke Abuja, mazauni ne na talakawa. Babu hanya mai kyau ko kwalta, amma akwai kananan otal marasa kyawu da dama a yankin.

Wakiliyar BBC Pidgin ta je daya daga cikin irin wadannan otel, ta iske kananan yara mata sanye da matsattsun kaya, yayin da wasu samari ke zaune a waje suna shaye-shaye.

Wakiliyar BBC ta nuna kamar cewa ita ma tana da kananan yara da take son ta kai su, su yi aiki a otel din.

Sai wanda ta iske ya ce mata ta zabi daki guda a cikin otel din inda za ta ajiye yaran idan ta zo da su.

Inda ya kara da cewa za ta rinka biyan kudi naira 10,000 a kowane mako. Sai ya ce mata idan yaran da za ta kawo din kanana ne, ta fada masu, su ce shekarunsu 20 ne ko kuma sama da haka.

Sun fada wa wakiliyar BBC cewa yaran da za ta kawo su rinka yin karuwancin za su rinka sama mata kudi tsakanin naira 10,000 zuwa 15,000 a kowace rana.

Shugabar hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya NAPTIP, Julie Okah-Donli ta shaida wa BBC cewa akwai kananan yara da yawa wadanda ake tursasa wa shiga karuwanci a Najeriya.

Ta ce “Matukar maza za su ci gaba da daukan karuwai, to kuwa za a ci gaba da sanya kananan yara cikin harkar karuwanci.”
Ta ce hukumar NAPTIP ta kama otel-otel da dama wadanda ake ajiye kananan yara domin karuwanci, ta rufe su kuma ta kai masu otel din kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *