Jarumar finafinan Hausa Fati Abdullahi  Washa ta lashe kyautar gwarzuwar jarumar matan Hausa fim ta 2019 a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka da aka gudanar a Landan, shi ne dalilin tafiyarsu Ingilan ita da abokan sana’arta da suka ki bayyana dalilin zuwan sai da aka gansu wajen bikin karramawar.

An ba da Sanarwar sunan Fati Washa ne a matsayin gwarzuwar jaruma a taron karrama ‘yan Fim da aka gudanar ranar Asabar a birnin London gaban dimbin jama’a masoya da mahalarta.

Bikin da ake kira Afro Hollywood Awards yana  karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma na Inglishi a sassan kasashen Afirka gaba daya.

Fati Washa ta lashe kyautar ne saboda rawar da ta taka a Fim din ‘Sadauki.’ Wanda ta taka rawar da bas aba gabi ba ta al’ada da saudakarwa da jajircewa.

A wurin karramawar Washa ta ari dabi’un Turawa da ta gudanar a wurin, ta fito ba mayafi, da ta je saman dandamalin ta mikawa wanda zai ba ta kyautar hannu sun gaisa, wadannan dabi’u sun sabawa Hausawa. Kuma ita tana wakiltar finafinnan Hausa a wurin.

Jarumar ta doke Aisha Aliyu Tsamiya a Fim din da ta fito “Jamila” da kuma Halima Yusuf Atete da ta fito a “Uwar Gulma”

Rahama Sadau ma ta samu wata kyauta a wurin yayin da Hadiza Gabon ita ‘yar kallo ce da rakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *