Spread the love

Zaman majalisar zartawa a duk sati ba dole ba ne ga dokar kasar Nijeriya tsari ne ga yanda jagoran gwamnati ya tsara ko kuma yanda ake son aminta da wasu manyan aiyukka na jiha ko kasa ba rashin zama ne abin Magana ko sabawa doka ba, aminta da wani babban aiki ba tare da an yi zaman ba.

Barista Mu’azu Liman Yabo ne ya yi wadannan kalamai don wayar da kan jama’ar Sokoto da ke Magana kan sabawa al’adar da gwamna Aminu Tambuwal ya gada, a gwamnoonin baya na zama taron majalisar zartarwar jiha duk ranar Larabar mako matukar ba a hadu da wani babban azuri da ya  bayyana ga al’umma ba.

Barista Mu’azu ya kara da cewar zaman ana yin sa ne saboda samar da yarda da amana tsakanin gwamnati da tallakawa amma fa ba dole ba ne rashin zaman, ba a sabawa doka ba, in akwai muhimman aiyukka da gwamnati ke son ta aiwatar za ta iya yin taron a wasu kwanaki jere har a kamala bayar da aiyukkan harka ce da ta shafi tasarin gwamnati. In ji shi.  

“Wannan abin bakinciki ne ace gwamnan da yasan  dokoki har ya jagoranci majalisa ya san muhimmancin taron majalisar zartarwa wadda ita ce hanyar tsara da inganta rayuwar jama’a da shardanta dokoki da sanin abubuwan da aka yi da yanda  za a dauki mataki ko gyara ga abubuwan da aka bayar, amma gwamna Tambuwal  ya jingine wannan tsarin”

“Ina kira gare shi da ya mayar da wannan zama na majalisar zartarwa da ake yi duk sati bisa al’ada domin mu san halin da kudinmu suke ciki da aiykkan da za a yi a jiha motsin talakawa ya ta’allaka ne ga yanda gwamnati ke bayar da kwangiloli da biyan ‘yan kwangila a sabbin aiki da tsofi amma shiru abubuwa ba su motsawa yanda ya kamata’ a cewar wani dan jihar Sokoto da ya nemi a sakaya sunansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *