Spread the love

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya ce za su tura ‘yan sanda dubu 66 da 241 a zaɓen gwamna da za a yi 16 ga Nuwamba a jihohin Kogi da Bayelsa.

Adamu ya faɗi haka a wurin taron kwamitin tsaro kan harkokin zaɓe wanda shugaban hukumar zaɓe Farfesa Mahmood Yakubu ya gabatar.

A cewasa ‘yan sandan da za a tura jihar Bayelsa su dubu 31,041.

Jihar Kogi kuwa za a tura dubu 35,200.

‘Yan sandan za su yi aikin kare mutane su tabbatar an yi zaɓe lafiya ba wata hatsaniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *