Spread the love

Mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce shirye-shirye sun kamala na gina jami’ar mata zalla, ‘ban son na furta wannan maganar ba a yanzu sai karshen wannan shekarar da zamu fito da yadda tsarin zai kasance na gina Jami’ar amma ba komai tun da dalilin yin hakan ya kama’.

Sarkin musulmin ya furta haka ne a shekarar 2014 da ta gabata wurin bukin kaddamar da littafai uku da Farfesa Sadiya Omar ta rubuta wadda take direkta ce a cibiyar Nazarin Hausa a Jami’ar Usman Dan Fodiyo dake Sakkwato, in da aka yi bukin a dakin taro na makarantar fasaha da kere-kere ta Ali Shinkafi  a Sokoto.

Mai martaba ya kara cewa Jami’ar za ta mayar da hankali wurin koyar da mata musulmi sha’anin kiyon lafiya domin a wannan kasar musulmi mata na fuskatar kalu-bale in suka tafi asibitoci kan wata matsala da ta shafe su, sai ka ga maza ne za su kula da su, wannan ya kara yi mana azama muka  ga lalle ba makawa sai mun gina wannan jami’ar don taimakawa ‘ya’ya mata na kasar nan baki daya.

Hakama ya kara da cewar Majalisarsa za ta ci gaba da taimakawa duk wani shiri na mata wanda zai kawo cigaba, domin sun san mata a kasar nan suna da kaifin basira musamman na yankin arewa, Malama Sadiya ta nuna mata na karatu da karantarwa a wannan yankin domin rubuta wadannnan littafai guda uku suna kara nuna mana yanda ilmin mata ya samu gindin zama a cikinmu. ‘Karantar da mata kamar karantar kasa ce gaba daya nan gaba kadan zamu fitowa  al’umma  yanda tsarin jami’ar mata zai kasance  a yanzu dai wasu mutane ne masu amana da dattako muka baiwa aikin kuma ana samun gagarumar nasara. cewar mai alfarma sarkin musulmi.

Sa’ad Abubakar ya kara da cewar majalisarsa tana nan tana kokarin bunkasa karantarwar mujaddadi in da sun kai a buga wasu  littafan Shehu a Kasar Masar don araba kyaauta ga jama’a, kuma ya kira ga Jami’ar Danfodiyo da ta fito da wani sashe a makarantar da za a rika bincike da sanin Daular Usmaniya. ‘Mun yi nisa wurin jawo masana ilmin fina-finai don a aiwatar da ingantacce kuma shahararren wasan kwaikwayo kan Daular Usmniya’. In ji sarkin Musulmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *