Spread the love

Jaruman Kannywood mata su uku abonkan juna sosai Rahama Sadau da Fati Washa da Hadiza Gabon sun tafi London don ganawa da sarauniyar Ingila kamar yadda Rahama ta faɗi a turakarta a dandalin sada zumunta na facebook.

Jaruman ba su bayyana dalilin zuwansu London ba, sai kawai ganin aka yi Rahama ta fito da wannan bayani da ake ɗauka raha ce take yi.

Jaruman suna cikin mata masu tashe a harkar kuma sun samu kuɗi a cikinta har ya sa suke sana’o’i daban-daban bayan harkar fim.

Magarciya duk yunƙurin da yi na sanin haƙiƙanin dalilin wannan tafiyar ba a samu nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *