Ta kowane  bangare ita manhajar ‘Qustodio’ tana da sauki domin mutum zai iya mallakarta a $55 domin sawa wayoyi har guda biyar, duk da akwai na kyautar shi amma ba komai da komai yake iya yi ba.

    

Mu sani akwai  manhajojin da an kirkere su ne  musamman domin iyaye, domin su taimake su wurin sanin abin da ‘ya’yansu suke ciki game da wayoyin da suke mu’amala da su a hannayensu a bayan idon mahaifa.

Idan yaronka ko diyarka  ya mallaki wayar komai da ruwanki (smartphone) sannan kuma yana iya samun damar siyan data da zai amfani da ita, wurin shiga yanar gizo (intanet) domin yayi bincike ko kuma sada zumunci a cikin shafukan sada zumunta  irin su Facebook ko Twitter ko WhatsApp, wasu iyaye kan ji dadi sosai har da sanar da abokansu irin wasa da wadannan na’urori da yaransu ke yi.

Amma iyayen da suke da tsabtacceciyar rayuwa hankalinsu ba ya kwantawa matukar akwai waya a hannayen ‘ya’yansu, musamman iyayen da suka san cewar wannan manhajar  ta  yanar gizo tana da wani bangare na gurbata tarbiya da kuma bangare na baiwa yaro samun damar da zai yi karatu da nazari, ga dauke hankali da tunani da ke hana samun damar hutawa domin yin barci.

Saboda wannan dalilai ya sanya wadansu kamfanoni suka kirkiro manhajoji na musamman wadanda ake kira da suna ‘Parental Apps’ wanda za a iya amfani da su domin sanin halin da yaransu ke ciki a halayyar duniyar gizo domin gyarawa ko karfafa yaronka.

 Manhajoji  suna da shahara da  birgewa iya ye za su iya gwada amfani da su na wasu kwanaki idan sun ga sun biya musu bukata, sai mutum ya siya wadda za ta zama mallakarsa. Manhajar za ta taimakawa   iyayen da suka mallakawa yaransu wayoyin ‘smart phones’.

‘Family Time’ manhaja ce da ta hada komai, domin tana iya baka damar tsara wayar yaronka abin zai samu damar amfani da shi, takaita mishi lokacin amfani da wayar, bibiyar wuraren da yake zuwa da  makamantansu. Ita manhajar za ta iya ba mahaifa damar su tsara lokacin da yaro zai rika yin aikin da aka ba shi a makaranta ya yi a gida watau  ‘Home work’ haka iyaye za su iya tsara lokacin da ake bukatar yaro ya kwanta yayi barci domin ya huta. Haka iyaye za su iya tsara wayar yaran na su iya lokacin da suke son su rika amfani da wayar da ke hannunsu.

Wani abun jin dadi da wannan manhaja ta FamilyTime shi ne kana iya saka wuraren da baka son yaronka ya je, misali ka ce baka son ya wuce daga unguwa ka za zuwa unguwa ka za, to da zarar yaron ya ketare dokar ka wannan manhajar za ta sanar da kai cewa yaron yana wuri ka za. Hakazalika a jikin manhajar akwai tracker wace za ta sanar da kai daidai inda yaron yake koda yayi batan dabo.

Daga cikin abin burgewa na wannan manhajar ta FamilyTime shi ne zai baka damar dakatar da kowane irin abun da ba ka son danka da diyarka su yi.

‘Qustodio’ manhaja ce mai dadin aiki da saukin fahimta kuma tafi dace wa da iyaye da ba su da cikakken lokaci ga yaransu. Tana da babban shafin da zai nuna maka duk abubuwan da suka faru a cikin wayar yaronka. Haka za ka san lokutan da yaronka ya bata wurin amfani da manhajoji kamar Instagram ko Twitter da sauransu.

Tun daga jikin wannan bangon zaka iya tsara tsawon lokacin da yaron zai yi amfani da wadannan manhajoji da kuma bincikan sakonnin da suke shigo mishi a waya, za ka iya dakatar da duk wasu gurbatattun shafuka da dakatar da kowane irin manhaja ta game da duk wata manhaja da uwaye  ba sa so.

Wannan su ne kadan daga ciki manhajojin da zamu kawo muku wanda za su taimaka wurin sanyawa yaranku idanu wurin amfani da wayoyin ‘smart phone’ da suke tare da su. 

Dukkansu zaku iya samunsu a ‘Android playstore’ naku.

Daga Shafiu Garba sokoto (Ict unit managarciya).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *