Spread the love

A daren jiya ne da misalin karfe 10:30, ‘yan bindiga, da ba a san ko suye ba suka shiga gidan Alhaji Lauwal Bakin Kasuwa in da suka yi nasarar tafiya da matarsa Hajiya Luba, daga gidan dake kan titin Kangiwa a GRA Katsina anan suka yi awon gaba da ita.

Hajia Luba, mata ce ga Alhaji Sani Lawal Bakin Kasuwa, wanda shi ne muƙaddashin mai ƙididigar kuɗi(accountant) na jihar Katsina.

Rundunar ‘yan sandan Katsina, a ta bakin kakakinta, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar wannan lamarin suna ƙoƙarin yanda za a san in da take har a maida ta cikin iyalanta.

Allah ya bayyanar da ita.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *