Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya taya shugaban ƙasa Muhammadu Buhari murnar nasarar da ya samu kan Atiku da PDP a kotun ƙoli ta ƙasa.

Tabuwal ya jinjinawa Alhaji Atiku Abubakar a jajircewarsa, ta yanda ya bi kadinsa yadda shari’a ta tanadar, matsayarsa bayar da gudunmuwa ce ga ɗimukuraɗiyar Nijeriya, ba tababa shi jagora ne a siyasar Nijeriya.

Yayi kira ga magoya bayan jam’iyar PDP su zama masu bin doka da oda kar su yi wata hatsaniya kan hukuncin da ya nuna an kawo ƙarshen rigimar shari’a.

Gwamna Tambuwal ya yi kalaman ne bayan kotun ƙoli ta yi watsi da shari’ar da ɗan takarar jam’iyar PDP Alhaji Abubakar Atiku, GCON ya ƙalubalance zaɓen shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Tambuwal ya taya Buhari murna ya yi kira gare shi ya mayarda hankali wajen kawo wa ƙasa cigaba da sauraren jama’a domin ‘yan ƙasa su morewa mulkin dimukuraɗiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *