Dan acaba mai shekara 42 mai suna Nonso Onyeje an same shi da laifi an kuma yanke masa shekara 14 gidan yari .

Babbar kotun Delta mai mazauni a Asaba ta kama shi da laifin yi wa wani karamin yaro dan shekara 9 fyade(Liwadi da shi), an boye sunan yaron.

Karamin yaron da kaddarar ta cika da shi dalibi ne a wata makarantar Firamari mai zaman kanta dake cikin hidikwatar Asaba.

An samu Onyeje da laifin da ake tuhumarsa, mai shari’a Ngozi Azinge a lokacin da take yanke hukuncin ta ce masu irin wannan laifin ba a yi masu sassauci domin wannan dabi’a ce ta rashin hankali da tarbiya.

Ta ce mutane irin wannan dan acaban yakamata a nisanta shi cikin mutane gudun kar ya bata yaran da ba su ji ba su gani ba. don haka duk mai bata al’umma ba za a sassauta masa ba.

Mai gabatar da karar Misis Uche Akamagwuna daga ma’aikatar shari’a ta ce laifin da ya aikata ya sabawa doka akwai hukuncin aka tanadar kan laifin karkashin sashe 214(1) a kundin dokokin jihar Delta.

Kwamishinan shari’a na jihar Peter Mrakpor ya ce duk wanda aka kama da laifin fyade dole a hukunta shi, gwamnati na yaki da hana fyade da cin zarafin yara kanana.

Ya ce gwamnati za ta cigaba da kare mutane marasa galihu kuma ba za a saurara ma duk wanda aka kama da laifin fyade ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *