Spread the love

                                  Daga Umar Bandi kofar kware.

        Matsalar tsabtar Muhalli matsala ce, da ta dade tana yi wa al’ummar kasashe masu tasowa barazana, duk kuwa kokarin da jama’a da gwamnatoci ke yi, na yunkurin magance wannan matsala,da ta dade tana haifar da matsalolin gurbacewar muhalli iri iri.

  A duk lokacin da ka zo kan matsalolin muhalli, musamman kan abin da ya shafi cunkushewar shara, a cikin lunguna a manya da kananan biranen mu, to ya zama tilas ayi maganar rawar da leda ke takawa, ta wannan bangare.

Hakika yana da kyau kafin mutsunduma kan warware zare da abawar yadda leda ke yiwa rayuwar al’ummar kasashe masu tasowa barazana, a wajen gurbacewar muhalli. Bari mu kalli yanayin sana’oin da ke taimakawa kan samun ambaliyar leda ko wane sako da lungunan muhallanmu.

   Daga farko dai akwai bakar Leda babba da karama, wanda mafi yawan ‘yan kasuwa ko masu tireda ke amfani da ita, a wajen inganta sana’oin su, ta hanyar amfani da ita a matsayin makunshinsu, masu amfani da nau’in leda da suka kunshi, masu sayar da kayan miya, kamar Timatur da makamantansu, da masu saida danyen nama da balangu a birane da kauyukka.

Haka kuma akwai leda fara babba da karama, wasu ‘yan kasuwa ke kulla shuga, gishiri, Tanka, magi da makamantansu, dukkanin wadannan nau’in ledodi, duk suna matukar barazana ga tabbatuwar tsabtar muhalli ga al’umma, wanda za’a ganinsu kusa a kowane lungu da sako, a birane da kauyukka a kan tituna da hanyoyi a cikin gidaje da gonakin tudu da fadammu,na noman rani da damina wanda ya zama babbar barazana ga gurbacewar mahallanmu.

A halin da muka samu kanmu, na ci gaban zamani musamman a birane, babu kamar ledar Pure water da ake kunsa ruwansha na sayarwa, wannan leda ta zama babbar barazana ga taimakawa a wajen tabbatuwar gurbacewar tsabtar muhalli, musamman yada ake dorawa kananan yara tallah ruwan pure water a tashoshin mota a kasuwanni a tituna da wuraren taruwar jama’a.

Wanda ya zama dalilin duk inda akaci ka suwa aka waste, ko akayi taro na siyasa ko wasanni ko na wayar da kan jama’a, zaka sami tarin irn wadannan ledodin na Pure water, wadan da aka yi ko oho da su, ba wani ko wasu jama’a da ke kallon irin illolin da suke samarwa a wajen gurbacewar muhalli, baya ga dinbin dattin da kuma irin tulin sharar da suka samar.

        Dake taimakawa wajen tushewar magudanun ruwa wuri daya wanda ke haifar da matsalolin ambaliya, tare da yaduwar Zazzabin cizon Sauro, ta hanyar baiwa Sauro mafakar da zai ci gaba da rayuwa yana nasa kwayakwansa yana kyankyashewa su zama barazana ga lafiyar al’umma, abin da ke janyo yawan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara.

Ledar tana matukar haifar da cikas ga manoma, ta hanyar hana tsirin shukarsu hudowa daga cikin kasa, da samun isashen ruwa da iska ga shuka, duk wadannan ababen na samuwa a dalilin leda kasancewar bata rubewa, baya ga mummunan abin da takewa Dabbobi, dake mutuwa a dalilin cin ledar.

Jama’a da dama na matukar bukatar ganin, an sami wani kamfani ko wata masana’anta da zata sarafa irin wadannan ledodin, wanda yin haka zai taimaka matuka, wajen rage irin barazana da illara da leda ke samarwa a wajen tabbatuwar tsabtar muhalli, tare da samar da aikin yi ga matasa idan aka sami masu sayen ledar musamman ledar Pure-water.

A yayin da wasu keda ra’ayin me zai hana a sanyawa masu kamfanin yin pure water su fito da wata hanyar kunshe ruwan su a cikin wani abu dake iya budewa a madadin leda, don a rage gurbacewar muhalli, ko kuma gwamnatocin jihohin da irin wannan ledar take da matukar yawa wajen samar da kamfanin dake iya sarafata zuwa wadansu abubuwa masu amfanin al’umma.  

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *