Spread the love

Babban Daraktan hukumar hana safarar bil’adama Julie Donly-Okah ta ce matasan mata miliyan uku ne ‘yan Nijeriya halin yanzu ke ciki sana’ar karuwanci a Nijeriya da wasu bangarorin duniya.

Donly-okah ta fadi haka ne a lokacin take gaban ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya domin kare kasafin kudin hukumarta a 2020.

Shugabar NAPTIP ta fahimci hukumarta na fama da kalubalen hana safarar mutane zuwa Turai da wasu bangarorin Afirika har da Nijeriya.

Ta ce yakin hana safarar bil’adama abu ne da yakamata a mayarwa hankali domin masu sana’ar suna da kudin da suke baiwa bata garin al’umma da masu fataucin kwayoyi a Nijeriya.

A cewarta safarar na damun hukumarta yanda take karuwa ana daukar yara zuwa Turai da gabas ta tsakiya a wuce da su cikin Afrika musamman Nijeriya.

Kididigar da ake da ita yanzu ta nuna ‘yan Nijeriya matasan mata miliyan uku ne ke karuwanci da wasu aiyukkan bauta a dukkan bangarorin duniya, akwai bukatar yin aiki tukuru don kawar da wannan batancin ga duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *