Spread the love

Kungiyoyin kwadago a Nijeriya sun tabbatar da za su hana kowane gwamna rawar gaban hantsi matsawar ya ki biyan albashi mafi karanci na dubu 30 da dokar kasa ta aminta abiya ma’aikatan gwamnati.

Wannan shirin yana karkashin jagorancin kungiyar kwadago ta kasa, sun ce ba su aminta da matsayar da gwamnoni suka cimma ba kuma ba su yi mamakin matakin gwamnonin ba na kin aminta su biya karancin albashin na dubu 30 don haka sun shirya musu.

Gwamnoni Nijeriya 36 karkashin jagorancin Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi sun yi zama a ranar Litinin suka ce biyan ya danganta da karfin jiha duk jihar da ba ta iya biyan dubu 30 za ta yi abin da yake maslaha a wurin biyan.

Aminta da fara biyan sabon albashin da majalisar zartarwa ta kasa ta yi ba ya nufin har da jihohi duk da majalisar ta umarci hukumomi masu kula da harkar karin su tura bayanan karin ga jihohi da kananan huklumomi.

‘Yan kwadagon sun ce ba su yarda da shirin na gwamnoni ba na kowace jiha ta biya kudin, daidai da kudin shigarta. Jiha ta biya yanda aka ba ta kudi a asusun tarayyar Nijeriya shi ne adalci. Ga kudin security votes da kudin jiha da wasu kudin kasashen duniya, a tattara kudin mana a gani ba su iya biyan albashin ne.

‘Yan kwadagon sun ce san sa kafar wando guda da jihohi har sun kaddamar da kwamitocin da za su rika sa ido ga abin da ake yi jihohi ba za su saurara ba har sai an biya kudin kamar yadda kungiya ta amince da gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *