Spread the love

Kutun daukaka kara ta Sauke Sanata Abubakar Shehu Tambuwal saman kujera Sanata mai wakiltar Sokoto ta kudu da Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin  Bodinga, Dange Shuni da Tureta Honarabul A.A Shehu dukkansu ‘yan jam’iyar APC ne.

Haka ma kotun ta bayar da umarnin Sanata Ibrahim Danbaba Dambuwa da Shehu Balarabe Kakale su haye kujerun dukansu ‘yan jam’iyar PDP ne.

Dukkansu sun daukaka karar hukuncin da Tarabunal ta yanke na watsi da korafinsu in da suka samu nasara yanzu.

Alkali Federich Oho a lokacin da yake yanke hukunci ya ce ya gamsu da korafe korafen masu daukaka kara, suna da gaskiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *