Spread the love


Kotun ƙolin Najeriya ta kori ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta Alhaji Atiku Abubakar suka shigar a gabanta don ƙalubalantar nasarar da hukumar zaɓe  ta bai wa shugaba Muhammadu Buhari a zaɓen 2019.Alƙalan kotun dai sun yi watsi da ƙarar ne bisa rashin dacewarta.Tun ranar 11 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙarar zaɓe ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar ta PDP ta shigar tana neman a soke zaɓen na watan Fabrairu.Kotun sauraron ƙarar zaɓen  ta yi watsi da ƙarar PDP don ta gaza gamsar da kotun kan ƙorafinsu da suke ganin an tafka maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa da iƙirarin  Buhari bai cancanci tsayawa takarar ba don bai mallaki shedar kammala sakandare ba.PDP ta kasa fito da hujjojin ita ta ci zaɓe.
Sakamakon zaben na watan Fabrairu dai ya nuna Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben da kashi fiye da 56 cikin 100 na kuri’un da aka kada.Wannan shi ne karon farko da kotun ƙoli ta yi watsi da shari’ar tun tashin farko ba a shiga shari’a gadan gadan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *