Spread the love


Alhaji Shehu Idris Sarkin Zazzau ya yabi ɗan wasan Hausa Adam A. Zango a hoɓɓasar da ya yi na ɗaukar nauyin yara ƙanana  101 su yi ilmi. Ya yi kalaman ne a lokacin da yakai masa ziyara.

Zango ya je fadar ne domin hannunta takardun cikewa domin shiga makaranta wato Fom na dalibai 101 da ya biyawa kudin makarantar.

Adam Zango ya raba Fom ɗin gida biyar: Masarauta, yan ɗarika, yan Izalah, jam’iyyar APC, da PDP. Yaran  za su yi karatu a makarantar Farfesa Ango Abdullahi International School dake garin Zaria a Kaduna.
Kamfanin shirya fina-finai na Adam Zango, watau ‘Price Zango Production Nigeria Limited’, ya biya makarantar miliyan N46.75 a mastayin kuɗin ɗaukar nauyin ɗaliban na tsawon shekaru uku.

Shugaban makarantar, Malam Hamza Jibril, ya tabbatar wa da manema labarai cewa jarumin ya biya kudin daukar nauyin daliban.

Zangon dai ya rufe bakin masu ganin maganar ba gaskiya ba ce don kowa ya san ɗan wasan ba zai yi wargi da mai martaba ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *