Spread the love

Ra’ayi:

WALANKENUWAR ADAMU ZANGO CIKIN MAGANAR DAUKAR NAUYIN KARATUN YARA.

Daga farko dai, tabbas ya kamata masarautun gargajiya musamman, su rika taka-tsan-tsan akan yadda za su yi hulda da mutanen da ba tsaransu a cikin hulda ba. Abu na biyu kuma, ban yarda Adamu ya yi hubbasar da muka zaci ya yi ba, kawai yana hadari gabas ne da hankullanmu, yana kuma ci gaba da kokarin boye karyar da ya kitsa, ta kuma tashi ba tare da an je nesa ba.

Yanzu Bari in Fara Rubutuna.

Yana da kyau a fahimci cewa, wannan rubutun na gina shi ne domin wadanda ke biye da wannan batun, saboda haka ba zan yi tiryan-tiryan ba ne. Sama-sama dai, domin bayyana matsayata.

  1. Da aka ce Adamu ya dauki nauyin yara 101 suyi karatu, aka ce ga takardar shaidar biyan kudi da kuma takardar godiya, kuma zunzurutun kudi har Naira Miliyan 46, tambayoyi da yawa sun kirkiri kansu, kuma duka suna bukatar a amsa su. Kadan daga ciki su ne;

A. Me yasa dalibai dari da daya? Anya a hankalce bai fi kamata ace dari cif ba?

B. Anya Adamu na da kudin da zai iya biyan Miliyan 46 cikin sauki haka?

Amma dai saboda kyakkyawan zato ga wanda ya aikata alkhairi, dukanmu sai muka shure kowacce irin tambaya da ke bijiro mana, muka ce Allah Ya sanya albarka.

Da gari ya waye, sai aka ce wani ya je makarantar, ya nemi ganin daliban, an ce ai ba su fara zuwa ba! Aka ce ai principal abokin Zango ne kuma kitsa wannan abin aka yi!! Aka ce daman Farfesa Ango ya tsawata akan cire sunansa daga wannan makarantar saboda rashin dattakon shugaban!!! Aka ce… Aka ce… Aka ce…

To a wannan gabar sai muka ce, an raba mana hankali biyu! Magabata irin su Jaafar suka tambayi Adamu ya nuna musu takardar banki da ke nuna cewa an biya kudin! Adamu yace shi don Allah yayi, ba zai nuna takardar ba. Ai shi ba dan riya ba ne. Ai shi dan Allah yayi.

Sai wasu ke cewa “to daga baya kenan”, idan har haka ne, tun farko me ya fito da wannan magana ta Instagram?

Daga nan kuma sai salon wasar ya canza. Aka ce ai daman yanzu ne za a lalabo yaran, an ba APC ta kawo mutum kaza, PDP mutum kaza, Masarautar Zazzau mutum kaza…

Babban abin mamaki shi ne, yadda wasu kusoshi na masarautar Zazzau suka bari aka yi wasa da hankalinsu, cikin kaddarar Allah har ga shi wasar ta kai gaban sarki.

Ban damu da wasa da hankalinmu da aka yi ba, ban kuma damu da lokacinmu da aka bata ba, amma na damu da cin zarafin masarautar Zazzau.

Ina ba sarki shawara, ya binciki wannan lamari daga farko har karshe, idan ya tabbatar an nufi wasa da shi ne, ya nuna shi ba abokin wasa ba ne. Idan kuma ya gano muna akasin sabon zatonmu, zan roki gafarar Adam Zango akan munana masa zato.

Nasiru Abbas Babi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *