Spread the love

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC ta kai samame a ofishin hukumar zaɓen jihar Sokoto in da ta kwashe wasu takardun muhimman bayanai kuma ta kama kwamishinan hukumar da jami’in kuɗi da wasu mutane da managarciya ba ta samu bayanan muƙamansu ba.

Majiya ta kusa ga hukumar ta ce bayan 12 na rana ne ma’aikatan suka zo ba su yi komi ba suka shiga ciki in da suka tafi da shugabannin wurin zuwa ofis ɗinsu dake kan titin sama domin amsa tambayoyi, har zuwa haɗa rahoton ba su dawo ba.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar zaɓe Malam Musa ya ce ba zai yi magana yanzu ba sai ya kammala samun bayani domin sanda managarciya ta kira shi a lokacin ya zo ofis.

Mai gadin hukumar ya sanar da manema labarai kowa ya zo zai shiga harabar hukumar a faɗa masa kar ya shiga cikin hukumar domin duk shugabannin wurin ba su ciki.

Jami’in hulɗa da jama’a na EFCC a jihar Sokoto Malam Mu’azu ya tabbatar da samamen ya ce da zaran sun kammala bincikensu za su sanar wa manema labarai.

Har yanzu ba’a samu cikakken bayanin dalilin kamen ba duk da wasu na ganin yana da alaƙa da kuɗin zaɓen 2019.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *