Spread the love

‘Yar wasan Hausa Samira Ahmed ta tallafawa uwayen yaro Al’amin da kuɗi Naira dubu 500 domin a cigaba da kula da lafiyarsa.

Managarciya ta samu bayani a wata majiya wannan tallafin jarumar ta saba yinsa. Bayan mutuwar aurenta ba a sake ganinta cikin fim ba amma koyaushe tana tare da mutanen Kannywood ɗin tana yin kasuwancinta da yin tallace-tallace ga kamfunna daban-daban.

Samira ta yi wannan taimako ba ta son kowa ya sani farincikin da mahaifin yaron ya shiga ne ya sa faɗa domin a san karamci na wannan matar.

‘Yan wasan Hausa musamman mata sun fito gadan gadan a wajen taimakon maras gata fili da ɓoye, kowace rana a yanzu sai ka ji wani abin farinciki na taimako da wata jaruma ta da ko wadda aka yayi ta aikata don gyaran rayuwar wani ko wata.

Taimakon da suke yi yana fama da yabo da suka a wurin mutane, ko yaya abin yake yakamata su daure a yi ta yi kar a huta aikin alheri ba a gajiya da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *