Jam’iyar adawa ta PDP a jihar Kogi ta ce rashin taron mutane a wajen kaddamar da yakin zaben APC da aka yi ranar Jumu’a data gabata don tunkarar zaben 16 ga watan Nuwamban 2019 ya nuna mutanen jihar Kogi sun sallami dan takarar jam’iyar APC Gwaman mai ci Yahaya Bello, sai ya fara tattara kayansa domin alamu ya nuna zai sha kaye.

Jam’iyar PDP a bayanin da ta fitar ta hannun sakataren yada labarunta Kola Ologbondiyan ya ce duk zargin da ake yi na jam’iyar APC na kokarin kawo tashin hankali da tarzoma amma jama’a ko a jikinsu sun yi tsayin daka sai sun sallami APC ga jagorancinsu..

Jam’iyar ta yi kira ga hukumar zabe da jami’an tsaro su tsaya kan gaskiya su dauki kowa nasu ne kar su yi son rai a lokacin zabe da bayansa.

Zaben jihar Kogi yana da zafi sosai yanda dukan jam’iyyun biyu APC da PDP suke da karfi da magoya baya, kuma kowanensu yana ganin shi ne zai lashe zaben ba da wata gardama ba.

Ganin yanda mutanen jihar suka karbi jam’iyar PDP duk da wasu naganin dan takararta ba shi ne al’umma suka so a zaba a zaben fitar da gwani ba, kabilarsa dake da rinjaye a jihar wadda ta dade tana mulkin jihar wannan zai iya yin tasiri a wurinsa ya hau kujerar Gwamna.

APC a matsayinta na wadda ke mulki tana da karfin da take iya rike kujerar domin kayar da mai mulki abu ne mai wahalar gaske duk da wasu mutane na ganin zaman Gwamna Yahaya dan kabila maras rinjaye a jihar zai iya sa ya sha kasa a zaben.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *