Spread the love

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Nijeriya yau kan ziyarar aiki a kasar saudiya a taron tattalin arziki.

Bayan taron Buhari zai tattauna da Sarkin Saudi Arebiya Salman da Sarki Abdallah ll na Jordan

A ranar Laraba Shugaban kasa zai sake halartar wani babban taro mai taken ‘Mi za a sake yi wa Afirika: Ta yaya za a saka hannun jari da dunke kasuwancin nahiyar yanda tattalin arzikinsu zai habaka a samu nasarar da ake so?’ Tare da shugaban kasar Kenya, Kongo-Brazzaville da Burkina Faso.

Bayan kammala taron a ranar Assabar ga Nuwamba Buhari zai wuce kasar Ingila a ziyararsa ta kashin kansa. Ana tsammanin ya dawo Nijeriya 17 ga Nuwamba na 2019.

Wannan bayanin yana kunshe ne a wata takarda da mai baiwa shugaban kasa sawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanyawa hannu ya rabawa manema labarai

Wannan fitar kenan Shugaba Buhari zai kwashe sati uku baya Nijeriya, dafatar ya dawo kasa lafiya.

Takardar ba ta nuna Buhari ya mika jagorancin kasa ga mataimakinsa kamar yadda ya saba ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *