Spread the love

Abin mamaki ya faru a garin Gano in da wani mutum Aminu Baita da aka ɗauka ya nutse a rafi ya mutu tun a shekarar 1990, shekara 30 da suka wuce sai ga shi ya bayyana ya dawo gida.

Wani na kusa da iyalansa, Yakubu Musa ya ce Aminu ƙwararren mai aikin jinya ne a asibiti ya samu matsalar ƙwaƙwalwa kafin ɓacewarsa daga gidansa da ke garin Danbatta, kilomita 70 daga birnin Kano a Arewacin Nijeriya.

Malam Musa ya ce sun ɗauka Aminu ya mutu a shekarun da suka wuce don bayan bayyana ya faɗa rafi ba su sake jin labarinsa ba kwata kwata.

“Kafin bacewarsa, Aminu yana aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar Kano a 1980s.”

“Bayan ya yi aure kwatsam sai ya fara nuna wasu halaye da ba a saba gani ba, hakan ya sanya rasa aikinsa kuma aurensa ya mutu a ƙoƙarin da aka yi na neman masa lafiya ba a kai ga nasara ba hakan ya faru.” in ji shi.

Ya ce an gaya masu a asibitin ɗanbatta ne Aminu ya sulale daga nan kuma ya daka tsalle ya fada rafi kuma ba a gano gawarsa ba. A matsayin suna musulmi sai suka rungumi ƙaddara.

“Kwatsam kuma sai lamari ya canja. Daya daga cikin yayye na, Nasidi Musa ya tafi karamar hukumar Toro a jihar Bauchi don neman wani surukinsa da ya bace da aka ce an gano shi a can.

“Da ya tafi bai gano sirikinsa ba amma sai ya gano ‘dan uwansa da ‘ya mutu, Aminu. “Nasidi ya dako shi sun dawo tare da labari mai ban mamaki.

A yanzu da na ke magana, Aminu yana asibitin kwakwalwa na Kazaure bayan an dawo da shi daga Toro.

“Abin mamaki shine bai manta sunan iyayensa ba da na kawunsa da har da mahaifi na. A lokacin da suke hanyar dawowa yana ta tambayar su.

“Mutanen garin da muka dako shi inda ya kwashe shekaru 30 yana zama ba suyi murnar rabuwa da shi ba. Labarin da muka ji shine ya zauna cikinsu kamar nan ne garinsu na tsawon lokacin da muke tunanin ba ya duniya.”

Lamarin nan akwai mamaki da kwance tunani cikinsa komine ne dai ya dawo gida hannun ‘yan uwansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *