Gidan Rediyon Ingila sashen Hausa ya fito da hanyar da za ta ƙara ƙarfafa harshen Hausa ga mata marubuta ganin yanda harshen ke bunƙasa a cikin duniya.

Wurin bukin karramawar ga waɗanda suka yi nasara a gasar rubutu ta #HikayaTa da BBC Hausa suka shirya, an gayyaci Zahra Buhari ‘yar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin ɗaya daga cikin manyan baƙi.

A al’adar buki bmanyan baƙi kan tofa albarkacin bakinsu don haka an buƙaci Zahra Buhari ta ce wani abu, sai dai ta baiwa mahalarta taron haƙuri, domin tafi iya turanci akan Hausa. Na yi mafi yawan rayuwata a kasar Burtaniya, a cewar Zahra Buhari.

Mutane sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan iƙirarin da Zahra ta yi na cewar ba ta jin Hausa sosai kamar yadda take jin turancin ingilishi.

Wasu na ganin ganin batunta gaskiya ne, wasa na ganin iya yi ne, ko mine ne dai shin tafi gwanewa kan turanci sama ga Hausa hakan laifi ne ga mutanen Arewa?

Wannan ne abin la’akari, kowa yasan yanda mutanen arewa ke wasa da harshensu da al’adunsu bai kamata su riƙe mutum ɗaya da laifi ba har in shi ɗin ne ya aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *