Fati Baffa Fage wadda aka fi sani da Fati Bararoji daɗaɗɗiyar ‘yar wasan Hausa ce da ta yi fice a zamanin can baya, ta fito fim irinsu Mashi, Tubali, Rawani, Sutura da Sunduki.

Bayan gama yayinta a duniyar fim ta cigaba da harkokin sana’arta har yanzu Allah bai kawo lokacin aurenta ba.

Kan haka ta ƙalubalanci masu faɗin sun ƙi aure da su zo su nemi aurensu in da gaske suke za su yi.

“To aure lokaci ne, kuma a yanzu ina nan Ina shirin yi da yardar Allah idan na samu miji ko yanzu a shirye nake da in yi auren, don wasu sai ka ji suna cewa mun tsaya ruwan ido ne, kuma ba haka ba ne, in da gaske su ke yi su masu fadar su fito su gwada mana.

In har da gaske suna son su aure mu din, don haka duk wanda Allah ya kawo mini, ni zabin Allah nake nema wanda zai so ni ya girmama iyaye na kuma ya rike ni amana.”In ji ta.

‘yan wasan Hausa sun yi ƙaurin suna a bakunan mutane cewa su zaɓar miji suke yi ba kowa ne suke so ba, sai wanda ya amsa sunansa namiji.

Mafi yawan mazan kuma kallon kitse suke yi wa rogo yanda suke ganin matan a fim cikin mayan gidaje da babbar sutura da mota a haka suke tsammanin su gansu a zahiri suna zuwa da zaran sun ga tabbas na rayuwar jaruma sai su ɓace ɓat ba a sake ganinsu.

Jarumman suna shan wuya ga mazan gari in aka fara maganar aure da zamantakewa ta gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *