Al’umar garin Zariya sun yabawa gwamnatin jihar Kaduna da majalisar karamar hukumar Zariya, kan fara bitar daftarin dokar da za ta hana saya da shan giya a unguwar da ake kira Sabon Gari.

A wata wasika mai dauke da kwanan wata 21 ga watan Okotoban nan ‘yan majalisar karamar hukumar Zariya sun gayyaci mai Otal da sauran wadan da ke sana’ar a wurin domin jin ta bakinsu.

Haka kuma sun gayyaci kungiyar Jama’atu Nasril Islam da kungiyar kiristoci, in da Alhaji Aminu Abdullahi da Fasto Moses Haruna suka wakilci kungiyoyin an sanar da su shirin da tabbatar da yin doka da ta da ce da kundin tsarin mulkin kasar Nijeriya.

Masu sayar da giyar sun yi kunnen uwar shegu da shirin sun tabbatar, su za su cigaba da sana’arsu domin doka ta ba su dama.

Wakilin masu sayar da Burkutu Mista Richard Sanka ya nemi a dakatar da shirin na yin dokar hana masu yin sana’arsu ta sayar da Burkutu, saboda da yawan zawarawan da suka dogara da sana’ar da ita suke ciyar da iyalansu. A cewarsa.

Lauyan masu Otal da masu sayar da giyar Mista Daniel Peter ya ce karamar hukuma ba ta da hurumin hana sayar da abubuwan ki da manyan ke amfani da su, suna dai da hurumin bayar da dama ko taikaita sayar da Burkutu.

Peter ya ce sashe na biyar dana shidda a daftarin dokar da ake kokarin tabbatarwa karara ya bayyana haramun ne sayarwa da shan giya, hakan kuma baya cikin karfin dokar ‘yan majalisar kowace karamar hukuma.   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *