Spread the love

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya farantawa talakawan Yobe rai ta hanyar raba musu kayan abinci, lamarin da aka wasu mutane a jihohin Arewa suka yaba.

Abin farinciki da annashuwa za ka g tsoho ya ɗauko buhun shinkafa a kansa zai kai gida ta zama mallakarsa, rabonsa da ya yi haka bai iya tunawa wani magidancin bai yaɓa yin haka ba tun da ya fara rayuwar aure.

Abinci a rayuwar aure shi ne jigon ɗaurewar zamantakewa cikin lumana da wasu gwamnatoci na fito da hanyoƴin da magidanta za su samu abinci da ƙila mutuwar aure da samun ɗiyan jama’a na gararanba saman titi da ya ragu.

Magidanta da matsan da suka samu gajiyar samun abincin ka ma daga shinkafa ko man dafuwa, sun shiga cikin farinciki da godiyar Allah ganin sun samu gwamnati da ta fara tausayinsu fata ya fito masu da hanyoyin dogaro da kai su riƙa samo abincin da kansu ba sai sun jira gwamnati ba.

Halin da talakawan Arewa suke ciki yakamata gwamnotoci su riƙa baiwa sha’anin walwala da jindaɗi muhimmanci domin da yawan wasu mutane suna faɗawa cikin halin laifi da aikata miyagun laifuka saboda ƙunci da rashin tabbas da suka shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *