Spread the love

Jihohin Nijeriya 36 ana biyarsu bashin Tiriliyan 3.6, a in da dukkansu kudin shigarsu da suka karba a shekarar 2018 Tiriliyan 1.1 ne, kamar yadda bayanan hukumar kula da bashi(Debt Management Offices) ta fitar.

Bayanan da aka fitar a Abuja ya nuna rancen ya wuce kudin da suke samu da naira Tiriliyan 2.5.

A bayanan jihar Lagas tafi kowace samun kudin shiga biliyan 382.18 bashin da ake biyarta ya kai naira biliyan 530.

Jihar Rivers ce ta biyu kudin shigarta biliyan 112.8 da bashin biliyan 225.6

Ogun tana hada naira biliyan 84, ana binta bashin biliyan 78.7 Jihar Delta da Kano biliyan 228.8 ana biyarsu bashin 117 da 58.4 da 44.1 a cikin shekara data gabata kowacensu.

Katutun bashin jihohin Sokoto, Neja, Jigawa, Anambra da Yobe ana binsu biliyan 176.9 amma kudin shigarsu a wadan nan jihohi biyar kadan ne sosai biliyan 62.1 suke iya hadawa gaba dayansu.

Rahoton ya nuna rabin shekarar nan jihar da tafi zama kasa a wajen karbar kudin asusun gwamnatin tarayya ita ce Osun ta karbi biliyan 10.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *