Biyo bayan yawan samun garkuwa da mutane a kauyukkan Abuja ‘yan ta’addan sun addabi wasu kauyukkan Kaduna da Sokoto hakan ya kara jefa tsoro cikin ma’aikatan gwamanati dake aiki a cikin birnin Abuja.

Abin da yakai ga wasu ma’aikatan sun rage zuwa garuruwansu yin hutun karshen mako gudun kar su fada homar masu yin garkuwa da mutanen.

Haka kuma Malamai da ake turawa kauyukka su karantar a wuraren da wadan nan lamari yake kazanta ana rufe makarantun da sauri don gudun kowane farmaki.

Wani ma’aikacin gwamnati ne a zantawarsa da manema labarai ya ce shi ya rage zuwa garinsu ne don yana gudun a sace shi, sanda komi yana lafiya lau duk ranar Juma’a sai ya tafi gida amma yanzu tun sanda lamarin ya kara ta’azzara a wajensu bai tafi ba.

Ya ce baya jin dadin rashin ziyartar kauyensu domin iyalinsa na can, saboda tsoron kar a yi garkuwa da shi.

Ya yi kira ga gwamanti ta dauki matakin da yakamata domin magance wadan nan mutanen bata gari a kawar da su a kauyukkansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *