A kalla kowace rana karamar asibitin dake kula da masu tabin hankali ta jihar Katsina jami’an lafiya dake wurin suna duba marar lafiya 50.

Yakubu Muhammad Saulawa jami’in kiyon lafiya ya ce bangarenmu na duba marar lafiya a kullum a kalla sai mun duba marar lafiya 50 wata ranar ma ana duba fiye da 100.

Muhammad Saulawa a lokacin da yake Magana kan cirutoci daban-daban da suka shafi tabin hankali a jihar.

Ya ce babban abin da ke jawo cutar tabin  hankali a jihar shaye-shayen miyagun kwayoyi ne.

Ya ce jihar nada karancin kwararrun masu duba matsalolin tabin hankali.

Mafiyawan matasan da ke karatun Likitanci a manyan makarantu daban-daban ba su son karatun bangaren duba masu tabin hankali.

Akwai abin da ake fada wanda ba haka ba ne wai in kana kula da mahaukata za ka zama kamar su.

Saulawa ya ce ba su da yawa a bangaren ba su fi su 20 ba dukansu a cikin jihar Katsina.

Ya yabawa gwamnati kan kokarin da take yi a haujin an samar musu da kayan aiki da gyara asibitocinsu.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *