Spread the love

M.A Faruk.

SHARHI.

KISAN DA SOJOJIN SAMA SUKA YIWA MATAR AURE DA MATASHI A MABERA, SAKKWATO.
-Yadda rayuwar Dan kudu tafi ta Dan Arewa daraja a yanzu.
Da ace a kudu ne sojoji suka yi wannan aika-aikar da yanzu manyan jaridu na gida da na waje sun buga labarin a shafinsu na farko! Da shugaban kasa ya dage zuwa kasar Rasha (Russia) ko ya tura wakilai suje jaje sannan tabbas sai Osinbajo yaje! Rayuwata tayi matukar ɓaci lokacin da naga labarin kisan gillar da sojojin sama dake da Bariki a unguwar  Nakasari cikin Sakkwato suka yiwa wata baiwar Allah da wani matashi a unguwar Mabera, abin takaici ma shine budurwar daya daga cikinsu ne ta kira su wai saboda an tsokane ta! Tsokana fa! Kamar yadda muke cewa a sakkwato ‘Tsarguwa’ ko ‘jan magana’. Shikenan suka ciko mota guda suka farwa mutanen unguwar a inda aka tsokane ta, da ta kasa nuna wadanda suka tsokane ta sai kawai sukayi kan mai uwa da wabi, suka rinka sa mutane tumamin kwado (frog jump) ba babba ba yaro har suka bi wani cikin gidan aure sukayi harbi! Mutun biyu suka mutu yayin da wasu suka samu munanan raunuka! Duk dai saboda wai an tsokani budurwar wani!
Abin farin ciki shine maigirma gwamnan sakkwato da ministan harkokin ‘yansanda duk sunyi ta’aziya ga iyalan mamatan kuma sunyi alkawarin daukar matakin da ya dace ta ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan ta’asar. Wani abin sha’awa shine yadda jama’ar sakkwato musamman a dandalin sada zumunta watau Facebook suka tashi tsaye da rubuta kalamai na ganin an dauki matakin daya dace.Tuntuni akwai labarai da dama na yadda sojojin saman ke gallazawa jama’a musamman masu abin hawa tsawon shekaru ba abinda aka yi.
A bangaren gwamnatin tarayya (Federal government) kuwa shiru kake ji! Ba Buhari ba, ba Osinbajo ba, balle su Garba Shehu. Idan zamu iya tuna yadda Buhari ya jajantawa iyalan Kolade Johnson, bayaraben da ‘yan sanda suka kashe a gidan kallo bisa kuskure a jahar ikko (Lagos) kwanakin da suka wuce inda nan da nan aka umurce kwamishinan ‘yan sanda na jahar daya kawo ‘yan sandan da sukayi kisan, labarin da name ba ku yanzu haka an kore su daga aiki! Wani misali bayan wannan shine kisan wani mai bautar kasa watau NYSC dake a channels TV lokacin zanga-zangar ‘yan Shi’a a Abuja. Osinbajo ya tashi daga Abuja har zuwa Kaduna inda mahaifan yaron suke yayi musu ta’aziyya tare da rakiyar gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-rufa’i! Yanzu an kashe mutun biyu a sakkwato birnin shehu amma ba wani jaje a bangaren gwamnatin tarayya! Saboda me? Mu kanmu bamu dauki Rayuwar ‘yanuwanmu hausawa da daraja ba, yanzu idan akace an kashe Dan arewa abinda zamu fara tambaya shine wacce Akida yake yi? Idan akwai banbancin Akida to babu ruwanmu!
A kudu ba ruwansu da banbancin Akidar kiristancinsu duk da suna Akidu barkatai a addinin kirista misalin manyan Akidunsu; darikar Katolika (Catholic),  Protestant, Orthodox, Jehovah da dai sauransu, amma kansu hade yake, duk da cewa akwai wadanda kwata-kwata basu bikin kirsimeti amma ba su fitowa suna zagin junansu.
Kwanakinnan aka gano masu satar yara suna maida su kiristoci a kano, hatta jaridunmu sun kasa watsa labarin yadda ya dace, malamanmu na addinu sunyi gum! Idan a kudu ne aka gano ana mayar dasu musulmai da tunj manyansu sun je wurin Buhari domin a dauki matakin gaggawa. Shekarun baya wata yarinya daga Bayalsa ta biyo wani matashi a Kano ta musulunta sukayi aure, nan da nan labarin ya zagaye Nijeria! Kana da labarin yanzu haka yaron mai suna Yunusa yana tsare a gidan yarin Bayalsa kusan shekaru biyar yanzu? Ba beli! Lauyan daya taimakawa yaron a lokacin shariarsa akayi masa barazana dole ya janye. Yanzu haka an turo lauyoyi daga jahar Anambara domin su amshi wadanda aka kama da satar yara a Kano!
Lokaci yayi da ‘yan Arewa zamu farka daga mummunan barcin da mukeyi! Idan muka dawo nan sakkwato kuma sai mu bawa gwamnati lokaci domin ta dauki mataki kamar yadda sukayi alkawari, sannan ko bayan daukar matakin, ya kamata a tashe su daga barikin Nakasari su koma a Isah, Goronyo ko Gandi ta karamar hukumar Rabah inda masu garkuwa da mutane suka addabi alumma, sai su nuna bajintarsu a can ba wai nan cikin gari ba akan marasa Karfi! Tunda  Sojojin sama ne suna da jiragen da ke shawagi a sama domin ganin masu garkuwa da mutane dake cikin daji suyi artabu da su.Allah ka jikansu da rahama ya kuma bawa Iyalansu hakurin jure wannan rashi.Allah ka agaje mu!

Margayi Abdussalam da sojoji suka harba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *