Spread the love

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta canja wa ma’aikatar sadarwa suna a zaman majalisar zartarwar ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa ya jagoranta.

Gwamnatin tarayya ta amince da canjawa mai’aikatar sadarwa wato ‘Ministry of Comuunications’ suna zuwa ‘Ministry of Communications and Digital Economy’ wata ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki da ya dogara a kan fasahar zamani.

Majalisar Zartarwa na kasa ta amince da canja sunan ma’aikatar sadarwa zuwa ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki da ya dogara a kan fasahar zamani.”

Daga yau sunan ya canja kuma haka za a riƙa kiransa a hukumance.

Shaikh Ali Isa Pantami yana kawo wa ma’aikatar sauye-sauye da cigaban zamani a harkar sadarwar duniya domin Nijeriya ta iya gogawa da takwarorinta a fannin kimiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *